Tambaya:
Assalamu alaikum, da fatan mallamai da dukkan 'yan uwa suntashi lafiya.
Ina rokon Mallam bayani kan hukuncin Wanda aka sanyama ranar aure kafin lokacin yace ya fasa.
Allah ya karama mallam lafiya da basira. Ameen
Amsa:
Wa alaikum assalam,in har akwai hujjar da sharia ta yadda da ita, ba shi da laifi in ya fasa,kamar ya bayyana budurwar ta sa ba ta da tarbiyya ko mazinaciya ce,ko kuma ba ta son shi,ko tana da cutar da za ta hana a sadu da ita,kamar toshewar farji ko hadewarsa da dubura, ko ya zama şu duka suna da jinin da in sun hadu za su haifi sikila, yana iya fasa auren idan ya zama ba shi da halin da zai iya ciyar da ita,ko kuma likita ya tabbatar maşa ba shi da mazakutar da zai iya saduwa da mace,haka ma idan ya ji ya tsaneta.
Dukkan abin da ake iya saki saboda shi, ana iya fasa aure ın aka same shi, an shar'anta saki ne saboda tunkude cuta daga ma'aurata ko daya daga cikinsu, yana daga cikin ka'idojin sharia da kuma masu hankali: Tunkude cuta kafin ta auku ya fi sauki fiye da kokarin kautar da ita bayan ta faru.
Allah ne mafi sani
Amsawa:
Dr Jamilu Zarewa.
Comments
Post a Comment