TAMBAYA:
Assalamu alaykum: Mallam ina bukatan shawara ko mafita in Allah yasa kanada masaniya akai.
Uncle dinane yakasance yakanyi mafarki dadare saiya ke razana wani lokaci ya tashi da gudu ko yake kai duka hakan wlh haryasa yakanji ciwo sosai.
Kuma yakanyi addu'o'i kamar karanta Kulhuwa, falaqi, Nasi, da ayatul qursiyu amma kuma abun yakan dameshi. Mafarkin yawani kamar macijine kebinsa.
Allah saka da alkhairi yakuna sa musamu mafita daga gareku ameen.
AMSA:
Wa alaikum assalam, Duk lo kaçın da ya yi mafarki ya razana ya dinga karanta addu'ar da ta tabbata daga Annabi s.aw. a hadisin Tirmizi mai lamba ta : 3528
أعوذ بكلمات الله التامات من غضبه وعقابه وشر عباده ومن همزات الشياطين وأن يحضرون
In har ya yi tofi sau uku a hagunsa ya canza bangaren kwanciyarsa, ba abin da zai cutar da shi, bayan haka.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa
Comments
Post a Comment