Tambaya
Assalamu alaikum, malam
Don Allah ina da tambaya? wai miye riba a musulunci? kuma idan mutum ya siyi abu nera 5 ya halatta ya sai da akan nera 8?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To malama riba ta kasu kashi biyu :
1. Akwai ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin naira hamsin, ka nemi ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren.
2. Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100 tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa 'yar gwamnati kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu.
Duka wadannan nau'oin guda biyu Allah ya haramta su, kuma ya kwashe musu albarka.
Amma idan mutum ya sayi abu naira 5, ya sayar naira 8, wannan ba'a kiran shi riba a musulunci, saboda yana daga cikin riibar da Allah ya halatta, saidai ana so mutum ya saukaka idan yana siyar da kaya, Annabi s.aw. yana cewa : "Rahamar Allah ta tabbata ga mutumin da idan zai siyar da kaya yake rangwame.
Allah ne mafi sani
Amsawa... ✍🏻
Dr Jamilu Zarewa
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment