Tambaya:
Dan Allah malam ina son ka yimin cikakken bayani game da Ilaa'i a shari'a.
Amsa:
To da farko dai shi ilaa'i a yaren larabci ma'anar shi kawai itace: Rantsuwa, kamar yadda yazo a cikin suratul-Nur aya ta 22.
Amma ma'ana shi a shari'a itace: mutum yayi rantsuwa kan cewa ba zai kara kusantar Matar shi ba ( ma'ana ba zai kara saduwa da ita ba) ,kamar yadda sahabi Abdullahi dan Abbas Allah ya kara mishi yarda yace: " mutum yai rantsuwa ba zai kara saduwa da Matar shi ba, to zata zauna tsawon wata hudu, idan kuwa ya sadu da ita to sai yayi kaffara, idan kuwa takai har wata hudu bai sadu da ita ba, shugaba ko alkali zai bashi zabi, kodai ya sadu da ita yayi kaffara ko kuma ya saketa, kamar yadda Allah ya fada a cikin suratu-Bakara aya ta 226 zuwa ta 227.
Don neman karin bayani sai a duba فتح القدير na ٳمام الشوكاني
Allah ne mafi sani.
Malam Anas Assalafy Fagge.
Comments
Post a Comment