Skip to main content

DUK YARAN DA MU KE HAIFA DA MIJINA SIKILA NE, ZAN IYA NEMAN YA SAKE NI NA AURI WANI?

Tambaya

Assalamu alaikum dafatan anwuni lafiya malam, dan Allah malam ina neman shawara ina da aure 'ya'yana ukku, na farko yana da 7yrs kuma yana da sikila na biyun yana da 5yrs sai ta ukkun nada 2yrs itama tanada sikila watanta biyar yanzu da rasuwa, sai dayan Wanda baida sikilar ya fara ceman kafarshi na ciwo ba ayi awaba kuma hannunwanshi suma suka fara ciwo, sai duka jikin shima ya dauki ciwo, shima mai sikilar sai ya.fara ciwan,.muna zuwa asibiti aka basu gado muka kwanta sun tambaye mu Wanda bai da sikilar mun yi mashi awo.ne mukace aa, saboda tunda akai haifeshi bai taba ciwo ba sai mura da dan zazzabi shima na rana dayane yawarke to sunyi mana bayanin cewa wata sikilar nadadewa
 kafin ta bayyana to sai ya rasu, shima dayan kwana daya da rasuwar wancen sai ya rasu kuma kanwarsu wata biyar tsakaninsu hankalina ya tashi yanzu banda 'ya'ya kuma ni kadaice wajen mijina, shi ya kuma fadi mani dole yakara aure ni kuma ya ce sai nan da shekara goma yake san in haihu ni.kuma inasan 'ya'ya kuma ina san mijina amma ban san in haihu da shi saboda na sha wahalar yara kuma jinin mune daya kaga dole tinani ya dame ni, shin zan iya cewa mijina ya sauwake mani inje insamu wani Wanda zan iya haihuwa yara ba sikila ba?? dan ALLAH inasan Karin bayani nagode

Amsa
Wa alaikum assalam 

Tabbas Kina cikin damuwa da tashin hankali, Tun da kin zama Mai wabi. 

Akwai hanyoyin likitanci na zamani da ake iya magance wannan matsalar ta haihuwar SIKILA, tare da cewa akwai tsada, Kuma ba Kowa ne zai iya ba, ita ya fi kamata ku fara bi in har za ku iya. 

In har ba ta mata magantu ba to Allah ya shar'anta saki ne Domin tunkude cuta daga daya daga cikin ma'aurata Ko dukansu Kamar yadda ayar Suratun Nisa'i ta tabbatar da hakan. 

Mutukar kin ga a cigaban zamanku akwai cutarwa kina iya neman rabuwa da shi Ko ta hanyar saki Ko fansar kai. 

Yana daga cikin manufofin aure samun zuriyya wadanda za su debe kewa. 

Idan Kuka rabu Allah zai iya azurta kowa daga falalarsa, ya ba ki miji ya kuma ba shi matar da in sun hadu ba za su haifi Sikila ba.

Allah ne mafi sani 

Dr. Jamilu Zarewa

Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...