Tambaya
Assalamu alaikum Dr. Yarinya ce tana da saurayi suna son junansu, amma saida aka zo ga6ar aure shi ne sai mahaifiyar saurayin take cewa ta shayar da mahaifiyar yarinyar nono, Malam yanzu don Allah ya matsayin auran na su zai kasance?
Amsa
Wa alaikum assalam, Babu aure a tsakaninsu, saboda ta zama 'yar 'yar'uwarsa ta bangaren shayarwa, 'yar 'yar'uwa kuma haramun ne a aureta kamar yadda Allah Ya yi bayani a aya ta (23) a Suratun Nisa'i.
Annabi (SAW) Yana cewa "Duk abin da yake haramta ta bangaren Nasaba, to yana haramta a bangaren shayarwa" kamar yadda ya zo a hadisin Bukhari da Muslim.
Ya wajaba iyaye sun dinga taka-tsantsan idan an shayar da yaransu, ko su rubuta su ajiye saboda ko da an yi auren dole a warware shi, kamar yadda ya faru da Ummu Yahya da Ukbah bn Harith a zamanin Manzon Allah (SAW) a hadisin da Bukhari da Muslim suka cimma daidaito wajan fitar da shi.
Allah ne mafi sani
Amsawa ✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment