Skip to main content

HIKIMOMIN DA AZUMI YA KUNSA

Tambaya

Assalamu alaikum Don Allah malam a taimaka min da bayani game da sababin da yasa ake yin azumi?? 

 Amsa

Wa'alaikum assalam Azumi ginshiki ne, daga cikin turakun musulunci, wadanda addinin musulunci, ba zai cika ba sai da su, Allah da manzonsa sun yi umarni da shi, saboda wasu muhimman manufofi, ga wasu daga ciki: 

1. Samun tsoron Allah, saboda mai azumi yana barin abin da yake so saboda Allah, hakan zai sa, ya kara samun tsoron Allah.

2. Samun kariya daga Shaidan, saboda azumi yana takure hanyoyin Shaidan, wannan ya sa zunubai suke karanci a Ramadan.

3. Tuna talakawa da wahalar da suke ciki, saboda duk lokacin da mai kudi ya dandana yunwa zai tuna halin da talakawa suke ciki.

4. Sabawa rai wajen barin abin da take so, da kuma hakuri akan abin da take sha'awa.

5. Kankare zunubai da kuma samun daukakar daraja, saboda azumi yana gyara zuciya, da kuma rai.

6. Samun lafiyar jiki, saboda azumi yana kariya daga cututtuka masu yawa, kamar yadda likitoci suka tabbatar da hakan.

7. Ta hanyar azumi mutum zai saba da yin aikin don Allah, saboda azumi sirri ne tsakanin Allah da bawansa.

Allah ne mafi sani. 

Amsawa:

Dr. Jamilu Zarewa.


Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...