Tambaya
ASSALAMU ALAIKUM
Game da tambayarka da ka yi akan matar da ta yi sabon-aure, ba tare da mijinta ya sake ta ba.
Bayan bincike da tambayar malamai, na isa izuwa ga hukunci kamar haka:
1. Abin da ta yi mummuna ne a shari'ar musulunci saboda ta yi aure cikin aure.
2. Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a matsayin mazinaciya take, saboda haka duk kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne.
3. Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu, 'ya'yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a baya.
4. Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har yanzu ita matarsa ce saidai idan ya sake ta.
5. Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare da sake daura aure ba, saidai dole sai bayan ta tuba, domin ita a matsayin mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren mazinaciya.
6. Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda girman zunubun da ta aikata.
7. Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san shari'a, domin ya yi musu hukunci.
ALLAH YA KIYAYE MU DAGA IRIN WANNAN AIKA-AIKAR.
Amsawa✍️
Dr. Jamilu Zarewa
Comments
Post a Comment