Tambaya:
Ina da tambaya akan sallah me raka'a Hudu zama biyu ( na tahiyya) amma wasu naga suna zama hudu, misali kamar idan anyi raka'a ta farko mikewa za'ayi amma se naga wasu sai sun zauna sannan su tashi meye hujjan wannan?
Amsa:
Yin hakan ya tabbata daga Annabi alaihis-salam kamar yadda Imamul-Bukhary da waninsa suka fitar da hadisi daga sahabin Annabi mai suna Malik binl-Huwairith Allah ya kara mishi yarda yace: naga manzon Allah alaihis-salatu was-salam idan ya kasance a wuturi a cikin sallah ( ma'ana raka'a ta farko ko kuma ta uku) baya mikewa tsaye har seya daidaita a zaune".
Wannan kuma itace abinda Imam Shafi'i ya tafi akai cewa mustahabbi ce a ruwaya mafi inganci daga gareshi, haka nan Imam Ahmad bin Hanbal kamar yadda Alkhallal ya rawaito daga gareshi.
Allah ne mafi sani.
Anas Assalafy Fagge.
Comments
Post a Comment