Skip to main content

MACE ZA TA IYA TAFSIRI DA LASIFIKA?

Tambaya
Mutane da yawa sun tambaye ni game da hukuncin tara mata a masallaci, mace ta yi musu TAFSIRI da lasifika ?

Amsa
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Yana cewa : "Duk lokacin da mutane suka hadu a dakin Allah suna kokarin fahimtar littafin Allah, nutsuwa za ta sauka gare su, kuma Mala'iku za su kewaye su, sannan Allah zai ambace su a wajan wadanda suke tare da shi". Muslim hadisi Mai lamba (7030).
Hadisin da ya gabata Yana nuna halaccin mace ta karantar da Alqu'rani a masallaci saboda hadisin bai bambance tsakanin namiji da mace ba.

Sai dai idan mun bi mazhabar malaman da suka inganta hadisin Amru dan Hazm akwai turnuku wajan mace ta yi Tafsiri a watan Azumi, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Yana cewa: "Kar Wanda ya taba Qur'ani sai mai Tsarki" domin Babu yadda za a yi mace lafiyayyiya mai matsakaitan shekaru, ta kammala Ramadhana uku ba ta yi AL:ADA ba.

Malaman Malikiyya suna fifita mace ta yi karatun Sallah a asirce har a sallolin da ake bayyanawa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarci mata da yin tafi idan liman ya yi rafkannuwa, idan suna tare da maza don kar aji muryarsu, kamar yadda Bukhari ya rawaito, wannan sai ya nuna ba a son mace ta daga muryarta, to ina kuma ga Lasifikar da za ta isar da sakon ga maza, ga kuma 'yan social media a gefe wadanda za su yada hotunanta da muryarta a duniya ?!!

Duk da cewa wasu daga cikin mata magabata suna koyar da maza da mata, sai dai ba a bainar Jama'a suke Yi ba cikin daga murya, wannan yasa yin kiyasi akan aikinsu ba zai tafi ba, saboda sababi da illar sun yi hannun riga.

Yana da kyau mata da maza masu yin Tafsiri su yi taka-tsantsan wajan fassara zancen Allah saboda darajar littafin da kuma girman dangantawa Allah abin da mutum ba shi da tabbas.

Ban da tafsirin Alqur'ani akwai hanyoyi da yawa na samun Lada.

Allah ne Mafi Sani

Dr. Jamilu Zarewa


Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...