Tambaya:
Assalamu alaikum
Allah Ya gafarta Malam wata tambaya muke da ita tambayar itace: Baba nah ne yake jinya tin last year besamu sauki ba,besamu yayi azumi shi ba har Allah yayimai rasuwa.shin zamu iya rama mashi ?
Amsa:
Wa Alaykumus Salam wa Rahmatullah
Idan azumin Ramadan ya riski wanda ke ciwon da a ke sa ran za a warke, sai ya sha azumin saboda ba zai iya yi ba, kuma bai samu lafiyar da zai iya ramawa ba bayan Ramadan har ya rasu, ba bu komai a kansa. Ba ramako, ba ciyarwa a kan magadansa. Dalili kuwa shi ne Shari'ah ta ba shi damar ya ajiye azumi saboda rashin lafiya. Tun da bai samu lafiyar da zai iya biyan azumin da ke kansa ba, ba wani wajabci a kansa ko magadansa.
Idan kuwa Ramadan ya riske shi a halin jinyar da ba a tunanin warkewa, wajibi ne ya ciyar da mabuqaci a madadin kowace ranar da bai yi azumi ba. Idan ba a ciyar ba har ya rasu, magadansa za su ciyar a madadinsa.
Idan kuma ya sha azumin ne a cikin rashin lafiyar da a ke sa ran zai warke, kuma ya samu sauqi bayan Ramadan, ta yadda zai iya rama azumin da a ke binsa, amma ya kasance bai yi ba har ya rasu, toh, magadansa za su yi azumin a madadinsa. Idan ba su yi azumi ba, za su ciyar.
Wallahu A'alam
Amsawar: ✍🏼
Sheikh Dr. Ahmad Bello Dogarawa
Daga: ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment