Tambaya
Salamun alaikum malam ina hukuncin wadda yana azumin nafila, sai sha'awa ta zo mai sai ya karya kuma ya sadu da matarsa?
Amsa
Wa alaikum assalam To dan'uwa malamai sun yi sabani game da wanda ya sadu da matarsa, alhalin yana azumin nafila, akwai wadanda suka ce sai ya sake, saboda ya bata aikinsa wanda ya faro. kuma Allah yana cewa: "Kada ku bata Ayyukanku" (Muhammad aya ta: 33).
Akwai malaman suka tafi akan cewa ba zai sake azumin ba, kuma ba shi da laifi. Wannan maganar ta karshe, ita ce daidai, saboda Annabi s.a.w. yana cewa: "Mai azumin nafila sarkin kansa ne, in ya ga dama ya cigaba da azumi, in ya ga dama kuma ya karya". (Albani ya inganta shi a sahihul-jami'i hadisi mai lamba ta: 3854).
Wannan hadisin sai ya nuna ba shi da laifi idan ya karya, karya azumi yana tabbata da cin abinci ko abin sha, ko jima'i.
Don neman Karin bayani duba Tuhfatul- Ahwazy 3/356
Allah Ne Mafi Sani
Amsawa ✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment