Tambaya
Assalamu alaikum warahmatullah
Allah ya karawa malan lpy dan Allah ga wata tmby daga wani dan uwa : Abokinmu ne ya rantse da kabarin iyayensa cewa baze dawo yayi aiki tare damu ba saboda wata matsala data shiga tsakani, to yanzu kuma yana so ya dawo muma muna so, yayi rantsuwar ne cikin fushi meye hukuncin kaffararsa zeyi azumi uku ne ko me zeyi??
Amsa
Wa alaikumus Salam
rantsuwa da kabarin iyaye ba ta inganta ba, duk wanda zai yi rantsuwa,ya rantse da Allah ko kuma ya yi shiru,kamar yadda ya tabbata a hadisi, rantsuwa da wanda ba Allah ba karamar shirka ce.
Ya dawo ya cigaba da aikinsa,ba ya bukatar kaffara,ya yawaita istigfari saboda abin da ya yi zunubi ne.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa
Comments
Post a Comment