Tambayoyin Ramadan /02
Tambaya:
Malam, wai akwai wani hadisi da yazo akan cewa annabi ya Kara akan raka'a goma Sha daya a sallan tarawihi?
Wai Idan babu, Idan mutum ya Kara akan Haka yayi laifi?
Shukran.
Amsa :
Wa alaikumus salam,
Eh, Lallai hadisi ya tabbata daga Ummul Mumimina Aisha Radiyallahu anha tace : "Annabi Sallallahu alaihi wa sallam bai taɓa yin sallah dare sama da raka'a sha ɗaya ba, cikin Ramadan ne ko a wajen Ramadan" wata ruwayar kuma ta zo yayi sallar dare raka'a sha uku, har da raka'atal fajri.
Waɗannan hadisai suna cikin Sihah da Sunan, wannan ya nuna Annabi Sallallahu alaihi wa sallam bai wuce raka'a sha ɗaya, in har akwai wani hadisin da ya nuna Annabi Sallallahu alaihi wa sallama yayi fiye da raka'a sha ɗaya to ni ban sanshi ba.
Amma idan mutum ya ƙara wurin sallar dare yayi fiye da raka'a sha ɗaya bai yi laifi ba, saboda hadisi ya zo Annabi Sallallahu alaihi wa sallama an tambaye shi game da sallar dare yace raka'a biyu biyu ake yi, in ka ji tsoron fitowar alfijir kan ka gama sai ka yi wutiri raka'a ɗaya. Don haka babu laifi wuce raka'a sha ɗaya.
Wallahu A'alam.
Amsawa
Abu Ahmad Tijjani Haruna
Comments
Post a Comment