SHIN ZAMU IYA YIN WANKA DA RUWAN ZAMZAM?
Amsa :
To dan'uwa ruwan zamzam ruwa ne mai albarka,
kamar yadda ya zo a hadisi cewa : Waraka ne ga
cututtuka, Suyudi ya kyautata shi a Jami'ussagir,
duba Faidhu Alkadeer 3/489.
Saidai duk da haka ya halatta ayi wanka da tsarki da shi a
zance mafi inganci , saboda ba'a samu dalilin da
ya hana hakan ba, ga shi kuma daga cikin
ka'idojin malamai duk abin da ba'a samu nassin
hani akansa ba a cikin mu'amalolin mutane, to ya
halatta.
Sannan sahabbai sun yi tsarki da ruwan da ya
bubbugo daga hannun Annabi s.a.w. , ruwan
zamzam kuma ba zai fi wannan ruwan daraja ba
.
Don neman Karin bayani duba : Hashiyatu Ibnu-
abiidin 1\180 da kuma Insaf 1\27.
DAGA DOCTOR JAMILU ZAREWA.
Comments
Post a Comment