Tambaya
Assalamu Alaikum Malam Auwal Dan Allah Gawata tambaya
Dan Allah mace tayi auri bada izinin babanta ba saboda Baya son auran ne Wani Yayan mahaifinta Yayi Mata waliyanci. Sai baban yace sai tarabu da mijin ta kuma suna da yara 3tana iya rabuwa da mijin ta. Saboda baba ta yace har tana gida mijin sai ya rasu katazo tako gidan shi wurin gaisuwa rasuwa. Na gode
Amsa
Wa'alaykumussalam
Baya halatta ga waliyyi ya hana abin waliccin sa auren wanda take so matukar ya chanchanci a aure a shari'an ce. Shi yasa manzon Allah ya tabbatar da a tambayi budurwa kafin aurar da ita a cikin hadisin bukhari 6968 da muslim 1419.
Baya halatta wani ya zama waliyyi matukar uba na nan, abinda akayi anyi kuskure amma ayi 'rafa'i'/ daga al'amarin zuwa ga alkali domin tabbar da shi a shari'an ce.
Wallahu A'alam
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment