Tambaya
Assalamu alaikum, don Allah a taimaka Mana da fatawa, a Jihar mu ta Nasarawa an fitar da umarnin hana sallar Jumu'a, shin
za mu iya kiran Sallah muyi Azahar a masallatan unguwar mu ?
Amsa
Wa alaikum assalam
Garuruwan da aka hana sallar Juma'a, aka yarda su yi Salloli guda biyar a cikin Jam'i, saboda hana yaduwar cutar Corona, ya halatta su yi Sallar Azahar a madadinta a cikin Jam'i a masallatansu su kira Sallah, su tada Ikama, saboda Malamai da yawa suna cewa duk wanda ya rasa Sallar Juma'a saboda wani uzuri karbabbe ko wanda yake yawan aukuwa ya halatta ya yi Azahar a cikin Jam'i a Masallacin da aka yi Juma'ar, tare da Kiran Sallah da Ikama, mutukar ba'a ji tsoran fitina ba ko kuma tunanin rashin cancantar limamin da ya jagoranci Sallar, Kamar yadda ya halatta ya yi a gida tare da iyalansa.
Don neman karin bayani duba: Almugny 2/99 da kuma Hilyatul-ulama'i Fi Ma'arifati mazahibil Fukaha'i na Kaffal 2/226.
Ya wajaba mu yawaita neman gafara a wajan Allah, saboda wasu lokutan idan zunubai suka yi yawa, Allah yana iya dakile bawansa daga aikin da zai kusantar da shi izuwa gare shi, Kamar yadda Allah ya yi bayani a suratu Attaubah aya (46).
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Comments
Post a Comment