Tambaya
Assalamu alaikum, Dr. Tambaya ce aka yi min, na ce bari na tambaye ku..
Idan mutun ya yi kisa na kuskure kuma ba ya da lafiyar da zai iya azumi, me ya kamata ya yi ?
Amsa
Wa alaikum assalam
Ya jira har ya samu lafiya ko kuma ya koma asalin kaffarar da ta wajaba ya Yi wato 'yanta kuyanga.
Babu zabin ciyarwa a cikin kaffarar kisan kuskure.
Allah ne mafi Sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment