Tambaya
Assalamu alaikum
Malam don Allah ina da tambaya.
Wani mutum ne ya auri wata mata, bayan sun rabu ya je ya auri 'yarta ta cikinta bisa rashin sani kuma dukkansu sun samu haihuwa da shi. To shin malam ya hukunci 'Dan da ya haifa na biyu shin shegena ko halattacena.??
Amsa
Wa alaikum assalam
In har Ya tabbata a rashin Sani ne, to za a raba auran, saboda Allah ya Yi bayani a suratun Nisa'i cewa: mutukar an kwanta da uwa, to 'ya ta haramta har abada, amma duka yaran da aka samu na sa ne, Babu shege a ciki !
Allah ne mafi Sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment