Tambaya
Assalamu alaikum warahmatullahi Wa barakatuh. malam Dan Allah a warware mana wannan matsalar..mutum ne ba lafiya aka nema masa taimakon kudi domin dashen qoda,ana cikin haka ba'a kai ga gamawa ba sai yarasu,to wannan kudin nasa ne ma'ana yazama nashi zai shiga gadonshi?ko za'a iya taimakon wani mai tsananin buqata irin wannan larurar.?mun gode jazakumullahu khairan.
Amsa
Wa'alaykumussalam
Dukiyar da wani ya bayar don mamaci, kafin ko a bayan rasuwar sa ne, ita ma ta na cikin dukiyar gado.
A duba : [FATA'WAL LAJNATID DA'IMA; 16/473]
Wallahu A'alam
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment