Tambaya
Assalamu Alaikum Doctor, ko menene ra'ayin ka game da tafsirul Maturidy na Abu-Mansur ?
Amsa
Wa alaikum assalam, Wannan tafsirin Abu-Mansur Almaturidy ne ya wallafa shi, ya rasu a shekara ta (333) bayan hijira, wanda shi ne jagoran wannan Akida ta Maturidiyya, manazarta da yawa sun yabi tafsirin ta fuskar Fa'idojin da ya kunsa, da tarin ilimin da yake ciki.
Saidai akidar Maturidiyya akida ce da ta yi kama da Akidar Asha'ira, sun yarda da siffofin Allah guda tawas kacal, sun yarda da siffofi bakwai wadanda Asha'ira suka tabbatar ta hanyar hankali, suna kuma kara sifar Attakwiin, ragowar sifofin kuma suna ta'awilinsu ko su kore su.
Mutum zai iya karanta tafsirin in har yana da duga-dugai tabbatattu a akidar ahlussunah, saboda zai iya zamewa !.
Bai kamata ayi muzakararsa da wani ba in ba zakakuri ba ne a Akidar Ahlisunnah, ko a fagensu don a dawo da shi kan daidai, haka nan karantar da shi a majalisai, saboda suna juyar da yawancin siffofin Allah daga ma'anarsu ta asali.
Allah ne mafi Sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment