Tambaya
Assalamu Alaikum malam Shin ya halatta in bawa kirista hayar gida?
Amsa
Wa alaikum assalam
Ya halatta a bawa kirista hayar gida saboda Musulunci Ya inganta yin mu'amala da kafirai kamar yadda ya Zo a suratul Mumtahanah.
Lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bude Khaibar ya bar wasu kasashenta a wajan Yahudawa Yana amsar rabin abin da ya fito na amfanin Gona kamar yadda Bukhari ya rawaito .
Allah ne Mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment