Tambaya
Assalamu Alaykum, Tambaya ta shi ne Malam zan Iya daukan kudin yarana marayu nayi jari dashi, saboda yaran nawaje na kuma banda abin hannuna dazan nayi musu wani uzirin dashi, ko sai na biyasu in na dauka.
Amsa
Wa alaikum as salam, ya halatta ga uwa ta yi amfani da dukiyar 'ya'yanta, a matsalolinta na yau da kullum,mutukar babu cutarwa, kuma ba wani za ta bawa ba.
Allah madaukakin sarki ya halatta cin dukiyar maraya ga wanda yake talaka,
kuma yake kula da ita, sai dai ya wajaba ya ci gwarwadon bukata, kamar yadda aya ta: 6 a suratun Nisa'i ta tabbatar da hakan.
Sai dai Allah ya san niyyar wanda ya yi nufin gyara, da wanda ya yi nufin barnatarwa, kamar yadda aya ta: 218 a Suratul Bakara ta nuna hakan.
Ayoyin da suka gabata, Suna wajabtawa masu kula da dukiyar marayu taka-tsantsan, duk wanda ya kiyaye dokokin Allah,tabbas Allah zai kiyaye shi, wanda ya cı dukiyar maraya da zalunci, tabbas yana cin wuta ne a cikinsa, Allah kuma zai saka shi a wutar Şa'ira.
Allah ne mafi sani
Dr jamilu Zarewa
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment