Tambaya
Assalamu Alaikum Malamina. Fatan Alkhairi a gareka, da fatan ka wuni lafiya cikin koshin lafiya. Malam dan ALLAH ina da tambaya kamar haka: (Mutum ne ya saki matarsa har saki (3) a lokuta daban-daban, to, sai wani bawan ALLAH yazo ya aure, bayan ya aureta sai wata matsala ta shiga tsakaninsu kuma ya saketa amma kuma ko sau daya bai taba sadu da ita ba, to, yanzu Malam ko wancen tsohon mijin nata zai iya mayar da ita, tun da gashi tayi aure amma saduwace kawai ba'a yi da ita ba???) ALLAH ya kara taimakon ka Malam.
Amsa
Wa alaikum assalam, ina har ba su sadu ba, to bai halatta ta auri wani ba, saboda lokacin da matar Rifa'ata ta auri wani bayan mijinta ya sake ta, ta so ta rabu da mijinta na biyun, ta koma wajan na farkon, kafin su sadu, Annabi s.a.w. ya hanata, inda ya ce mata : "Dole sai kin dandana dadinsa, shi ma ya dandana dadinki", kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta:5372, wannan sai ya nuna cewa aya ta : 230 a Suratul Bakara, ba aure kawai take nufi ba, tana nufin aure hade da saduwa su ne suke halatta mace ga mijinta na farko, saboda aikin Annabi s.a.w. da maganarsa su ne suke fassara Alqur'ani.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment