Tambaya
Assalmu alaikum malam tambayana shine ina rama azumina a litinin da Alhamis yayi? Ammafa nayi sittu?
Amsa
Wa alaikum as salam,an yı sabani game da yın sittu shawwal kafin a gama ramuwar Ramadan, zance mafi inganci shi ne : ba za'a yi ba, saboda Annabi (s.a.w)a hadisin Müslim ya sanya ladan sittu shawwal ne bayan kammala Ramadan.
Za ki iya rama azumin Ramdhana ranar litinin da alhamis, saidai ba za ki samu ladan su gaba daya ba, saboda manufar su ta banbanta, saboda ko da ace ibadoji Iri daya ne, in manufar su ta banbanta kowacce za ta ci gashin kanta, wata ba za ta wakilci 'yar'uwarta ba.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa ✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment