Skip to main content

ZAN IYA ZAMIYAR BASHINA DAGA ZAKKA ??

Tambaya

Assalamu Alaikum. ya sheikh. Ina da tambaya. Idan ina bin mutum bashin kudi kuma zanyi zakka, zan iya cewa na bar mai abinda nake binshi a matsayin zakka?

Amsa
Wa alaikum assalam

Malamai sun yi sabani a wannan mas'alar zuwa zantuka guda biyu:

1. Ba ya halatta mutum ya mayar da bashin da yake bin wani a matsayin zakka, saboda Zakka hakkin Allah ne, yin hakan kuma zai zama ya amfanar da kansa da zakkar saboda in ba ta hanyar ta ba da kudinsa ba za su fito ba, Wannan ita ce fatawar Malaman Hanafiyya da Hanabila sannan kuma ita ce fatawar malaman Malikiyya in ban da Ash'habu, hakan kuma shi ne mafi inganci a wajan Shafi'iyya. 

2. Ya halatta ya mayar da bashinsa da yake kan wani ya zama Zakka, saboda in da zai ba shi zakkar ya dauke ta ya biya shi bashi da ita da ya halatta ya amsa, wannan ita ce fatawar Ash'habu daga Malikiyya sannan kuma Kauli ne a mazhabar Shafi'iyya kamar yadda Nawawy ya ambata a Almajmu'u.

Don neman Karin bayani duba: Almausua Alfiqhiyya 23/131.

Duk da cewa babu nassi yankakke bayyananne a mas'alar a iya bincikenmu, Saidai fatawar manyan malamai na rashin yin ZAMIYAR ita ce ta fi rinjaye, saboda kubutar da wuyaye daga yiwuwar kuskure yana da kyau sannan fita daga sabanin Malamai abin so ne.

Allah ne mafi sani 

Dr, Jamilu Zarewa


Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...